1 Corinthians 12

1Game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki ‘yan’uwa, bana so ku zama da jahilci. 2Kun san cewa lokacin da ku ke al’ummai, an rude ku da alloli marasa magana ta hanyoyi dabam dabam marasa kan gado. 3Saboda haka ina so ku sani babu wanda ya ke magana da Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne.” Babu kuma wanda zaya ce, “Yesu Ubangili ne,” sai dai ta Ruhu Mai Tsarki.

4Akwai bay bye iri iri, amma Ruhu daya ne. 5Akwai hidimomi iri iri, amma Ubangiji daya ne. 6Akwai aikace aikace iri iri, amma Allah daya ke bayyanawa kowane mutum yadda zai aiwatar da su.

7To ga kowanne an bayar da ikon nuna ayyukan Ruhu a fili domin amfanin kowa. 8Ga wani ta wurin Ruhu an bayar da baiwar hikima, kuma ga wani kalmar sani ta wurin Ruhu daya.

9Ga wani an ba shi baiwar bangaskiya ta wurin Ruhun nan, ga wani kuwa an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhun. 10Ga wani yin ayyukan iko, ga wani kuwa annabci. Ga wani kuwa an ba shi baiwar bambance ruhohi, ga wani harsuna daban daban, kuma ga wani fassarar harsuna. 11Dukan wadannan Ruhu daya ne ya ke iza su, ya kuma rarraba baye bayen ga kowannen su yadda ya nufa.

12Kamar yadda jiki daya ne amma da gabobi da yawa kuma duk gabobin na jiki daya ne, haka nan Almasihu yake. 13Gama ta Ruhu daya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki daya, ko Yahudawa ko al’ummai, ko bayi ko ‘ya’ya, dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu daya.

14Gama jiki ba daya ba ne sungun, amma gabobi ne da yawa. 15Idan kafa ta ce, “tun da dai ni ba hannu ba ne to ni ba fannin jikin bane,” wannan baya rage masa matsayin sa a jikin ba. 16Kuma da kunne zaya ce, ‘‘’Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gabar jiki ba ne,‘’ fadar haka ba za ta raba shi da zama gabar jikin ba. 17Idan dukan jikin ya kasance ido ne da me za a ji? Da dukan jikin kunne ne, da me za a sunsuna?

18Amma Allah ya shirya gabobin jiki bisa ga tsarin sa. 19Amma da duk jiki gaba daya ce, da ina jikin zai kasance? 20Ga shi akwai gabobi da yawa, kuma jiki daya ne.

21Ba da ma ido ya fadawa hannu, ‘’Bana bukatar ka,‘’ ko kuma kai ya fadawa kafafu, ‘’Ba na bukatar ku.‘’ 22Amma, sai ma gabobin da ake gani kamar raunannu su ne masu humimmanci, gabobin jiki kuwa da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mu kan fi ba su martaba. 23Ta haka gabobinmu marasa kyan gani, akan kara kyautata ganinsu. Gabobin mu masu kyan kuma ba sai an yi masu ado ba. 24Amma Allah ne da kansa ya hada jiki, yana bada mafificiyar martaba ga kaskantacciyar gaba.

25Yayi haka ne domin kada a sami tsattsaguwa a cikn jikin, amma domin gabobin su kula da juna da matsananciyar lura. 26Kuma idan gaba daya na wahala, dukan gabobin suna wahala tare. ko kuma idan an girmama gaba daya, dukan gabobin na farin ciki tare. 27Yanzu ku jikin Almasihu ne, saboda haka kuma kowannen ku gabarsa ne.

28A cikin ikilisiya, Allah ya sa wasu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa’an nan sai masu yin ayyukan iko, sai masu aikin warkarwa, da masu bayar da taimako, da masu aikin tafiyar da al’amura, da masu harsuna daban daban. 29To kowa manzo ne? ko kuwa duka annabawa ne? ko kuma duka masu koyarwa ne? Kowa ne ke yin manyan ayyukan iko?

30Ko kuwa dukan su ne suke da baiwar warkarwa? Dukan su ne ke magana da harsuna? ko kuma dukan su ne ke fassara harsuna? Amma bari ku himmantu ga neman baiwa mafi girma. Kuma zan nuna maku wata hanya mafificiya.

31

Copyright information for HauULB